Mista Ban ya bayyana cewa, kudurin da aka tsayar ya kasance wani babban ci gaba a kokarin daidaita rikicin kasar ta hanyar shawarwari da dabarun siyasa, sa'an nan yana son ganin kungiyoyin dake adawa da gwanatin kasar Syria sun gaggauta wajen kafa wata tawagar da za ta wakilci dukkansu wajen wannan taron.
Kungiyar NCSROF ta sanar a ranar 18 a birnin Istanbul na kasar Turkiya da cewa, za ta halarci taron Geneva na 2 kan Sham da za a kira a ranar 22 ga wata. (Bello Wang)