Gwamnatin Sham da 'yan adawa sun ci gaba yin shawarwari a fadar 'Palace of Nations' dake birnin Geneva a ran 26 ga wata. Wakilin musamman na MDD da kungiyar kasashen Larabawa kan rikicin Sham Lakhdar Brahimi ya bayyana cewa, gwamnatin Sham tana maraba da matakin ficewar mata da yara dake birnin Homs daga yankunan da sojojin kasar suka kewaye nan take.
Ko da yake gwamnatin Sham ta bukaci a tantance su kafin su bar wadannan yankuna. Malam Brahimi ya ce, mai yiyuwa ne daga ranar 27 ga wata, mata da yara za su iyar ficewa daga birnin Homs, yana fatan sauran fararen hulu za su iyar samun wannan dama. Ban da wannan kuma, Malam Brahimi ya yi nuni cewa, a halin yanzu dai an riga an shirya kayayyakin ba da agaji, yana fatan za a isar da su cikin gaggawa zuwa birnin Homs a ran 27 ga wata. (Danladi)