Kakakin MDD ya sheda ma manema labarai a jiya Litinin 27 ga wata cewa, an yi jigilar karin kayayyakin makaman nukiliya daga kasar Sham domin a lalata su.
Mataimakin kakakin babban sakataren MDD Farhan Haq ya bayyana cewa, bayan jami'an MDD sun sa ido kan wadannan kayayyaki, za'a jibge su a cikin wasu jiragen ruwa masu daukar kayayyaki na kasar Denmark da Norway a mashigin teku na Latakia.
Ya ce jiragen ruwan yaki na kasashen Sin, Denmark, Norway da Rasha sun ba da kariya ga jiragen dake dauke da makaman. Ban da haka wakilin MDD ya nuna fatansa na ganin kasar Sham da ta kara yin kokari domin kawar da makaman nukiliya cikin lumana da lokaci. (Amina)