Brahimi ne ya kira shawarwari a wannan karo kuma ya jagoranta. An ba da labari cewa,tun a jiya ne tawagogin bangarorin biyu suka isa birnin Geneva. Ministan harkokin wajen kasar Syria Walid Al-Moallem shi ne ya jagoranci tawagar gwamnati, yayin da yawancin mambobin tawagar 'yan adawa sun fito daga kungiyar adawa mafi grima wato NCSROF. A wannan rana da muke ciki, Brahimi ya gana da shugabannin tawagogin biyu da kansa domin tabbatar da ajandar taron a wannan karo da abubuwa da za a tattauna a taron da sauransu. Sai dai babu tabbaci ko za su yi shawarwari a wannan rana kai tsaye ko a'a.
Ban da haka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana a yau Litinin 10 ga wata a nan birnin Beijing cewa, Sin na maraba da shawarwarin da bangarorin biyu suke yi a wannan karo, tare kuma da yin kira da su nace ga hanyar warware rikici ta hanyar siyasa, ta yadda za a samu wata hanya da ta dace domin kau da bambancin ra'ayi da suke da shi . (Amina)