Ran 27 ga wata ta zama rana ta uku da gwamnatin kasar Sham da gamayyar kungiyoyin adawa na kasar suke ci gaba da kokarin shawarwari a tsakaninsu. Yayin da yake sanar da sabon ci gaba da aka samu daga shawarwarin a ran 27 ga wata, wakilin musamman na MDD da na kungiyar kasashen Larabawa kan batun rikicin Sham Lakhdar Brahimi ya bayyana cewa, a halin yanzu bangarorin biyu basu cimma ra'ayi daya ba tukuna kan batun shigar da aikin jin kai cikin birnin Homs.
Malam Brahimi ya ce, a shawarwarin ranar 28 ga wata, bangarorin biyu za su mai da hankali kan sanarwar Geneva, tare da tattaunawa kan muhimman abubuwan da ke cikin wannan sanarwa da yadda za a gudanar da su, ciki har da batun kafa hukumar wucin gadi mai cikakken iko.(Danladi)