in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tattauna aikin ceton jin kai a Sham a ranar 25 ga wata
2014-01-26 10:46:40 cri

Wakilin musamman na MDD da kungiyar kasashen Larabawa kan batun rikicin Sham Lakhdar Brahimi ya bayyana a ran 25 ga wata cewa, a gun shawarwarin da gwamnatin kasar Sham da 'yan adawa suka yi a wannan rana a daki guda, an mai da hankali kan aikin ceto na jin kai.

Malam Brahimi ya yi nuni a gun taron manema labaru da aka shirya bayan shawarwarin cewa, ya yi shawarwari da wakilan bangarorin biyu na Sham sau biyu, inda suka tattauna kan ba da taimakon kaya na jin kai, ciki da abinci da magunguna ga yankin Homs na kasar Sham. Ko da yake ba a samu babban ci gaba a gun shawarwarin ba, amma bangarorin biyu sun yi musanyar ra'ayoyinsu ta bakinsa, wannan dai wani mafari ne mai kyau, za a ci gaba da yin shawarwarin a tsakaninsu.

Rana ta 25 ta zama rana ta farko da gwamnatin Sham da 'yan adawa suka yi shawarwari a cikin daki guda, tawagogin shawarwarin suna karkashin shugabancin zaunannen wakilin Sham da ke MDD Bashar Jaafari da manyan jami'an gammayar kungiyoyin adawa na kasar.

Malam Brahimi ya kara da cewa, kasar Sin ta gabatar shawarwari guda 5 wajen daidaita matsalar Sham bisa matsayinta na kasa dake da kujerar din din din a kwamitin sulhu na MDD, da kuma babbar kasa mai girma a yankinta. Yana ganin cewa, kamata ya yi kasashe 5 da ke da kujerun din din din na kwamitin sulhu na MDD su bayar da amfaninsu, domin maido da zaman lafiya a Sham. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China