in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
`Yan kasar Sham kimanin miliyan 6.5 ba su da tabbacin samun isashen abinci
2014-01-15 14:22:10 cri
Kakakin hukumar tsara shirin samar da abinci ta duniya wato WFP Madam Elisabeth Byrs ta bayyana a gun taron manema labaru da aka yi a ran talata 14 ga wata cewa, saboda rikicin da ya barke a kasar Sham, 'yan kasar kimanin miliyan 6.5 ba su da tabbacin samun isashen abinci.

Madam Byrs ta bayyana cewa, samarwa 'yan kasar kimanin miliyan 4 da dubu 250 da 'yan gudun hijira na kasar miliyan 2 da dubu 900 wadanda suka gudu zuwa sauran kasashe, kalubale ne kuma wani aiki dake cikin gaggawa ga hukumar WFP. Tana mai cewa, hukumar na bukatar kudi dala miliyan 35 a ko wane mako domin biyan bukatun wadannan mutane, don haka ana bukatar samun tallafin da ya kai dala biliyan 2 a wannan shekara domin samar da abinci ta yadda za a samu damar sasanta halin da ake ciki a kasar.

Ban da haka, hukumar na nuna damuwa sosai kan lafiyar jikin 'yan kasar Sham da rikicin ke dabaibaye, ganin yadda ta yi iyakacin kokarin samar da tallafi ga mutanen dake kewaye da birnin Damascus a watannin da suka gabata, amma ba ta cimma nasara ba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China