in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu ci gaba a yayin taron Geneva karo na biyu
2014-01-27 20:11:08 cri
Ranar 27 ga wata bisa agogon birnin Geneva, wakilan gwamnatin kasar Sham da na 'yan adawa suna ci gaba da shawarwari a tsakaninsu a karkashin kulawar Lakhdar Brahimi, manzon musamman na hadin gwiwar MDD da kungiyar kawancen kasashen Larabawa kan batun Sham, inda suka mai da hankali kan batun jin kai da sauran batutuwa.

Wannan shi ne karo na farko da gwamnatin Sham da masu adawa da ita suka yi shawarwari keke da keke tun bayan barkewar rikicin Sham, lamarin da ya samar da yiwuwar sa aya ga tashin hankali da warware rikicin a siyasance. Ban da wannan kuma, gamayyar kasa da kasa sun bayyana ra'ayoyinsu da murya daya kan yadda za a warware rikicin, wato ya zama dole a warware rikicin na Sham a siyasance, a maimakon daukar matakin soja.

Ana ganin cewa, ko da yake ya zuwa yanzu bangarorin 2 na fuskantar wasu sabane-sabane, amma akwai alama mai kyau ta ci gaba da taron. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China