Wata majiya daga ofishin watsa labarai na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva ta bayyana haka ga wakilin Xinhua, kamfanin dillancin labarai na kasar Sin, inda ta yi bayanin cewa, bangarorin 2 a halin yanzu suna tattaunawa tare da manzon musamman mai kula da batun Sham mista Lakhdar Brahimi, a ofishin MDD dake Geneva.
Hakan ya zama karo na farko ke nan da bangarorin 2 suka gana gaba da gaba a shekaru 3 da suka wuce, duk da cewa sun nuna shakku lokacin da aka fara taron Geneva karon na 2 a ranar Laraba a Montreux na kasar Swiss. (Bello Wang)