Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya jagoranci wannan taro, inda ya yi jawabin a gun bikin bude taron cewa, shekaru uku bayan aukuwar rikicin kasar, karo na farko ke nan da gwamnatin da kungiyoyin adawa na kasar Sham da kuma wasu kasashe dake da alaka da wannan batu da sauran kasashen duniya suka yi taron domin fidda wata hanyar siyasa da za a bi don warware wannan batu, hakan ya nuna wata alama mai yakini ga warware wannan batu. Ya kara da cewa, jama'ar kasar sun dauki muhimmin nauyi wajen magance rikicin kasar da yanke shawara kan tsare-tsaren siyasa har ma da makomar kasar, don haka ya kamata, kasashen duniya su yi iyakacin kokarin tabbatar da muraddunsu.
Ministan harkokin waje na kasar Sin Mr Wang Yi wanda ke halartar wannan taro a cikin jawabin sa ya ce, ya kamata, bangarori daban-daban da wannan batu ya shafa su bayyana fatansu a siyasance da yanke shawara a wannan batu, tare kuma da nacewa ga hanyar warware rikicin kasar ta hanyar siyasa da koyi da sauran fasahohi masu amfani, ta yadda za'a zabi wata hanya da ta dace bisa moriyar kasar da yin la'akari da bukatun bangarori daban-daban.(Amina)