in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane da dama sun yi asara sakamakon harin bom da aka kai a Lebanon
2014-01-03 14:05:44 cri

Wani bam da aka dasa a cikin mota ya fashe a ranar Alhamis din nan 2 ga wata a Beirut cibiyar kasar Lebanon, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4 yayin da wasu 77 suka jikkata.

An ba da labarin cewa, a wannan rana da misalin karfe 4 da maraice, wata mota da aka dasa bam a ciki ya fashe a karkarar dake kusa da Beirut inda mutane suka yi cincirindo. Abin da ya kasance harin bam da aka kai karo na biyu a kasar cikin mako daya.

Shugaban kasar Michel Suleiman ya ba da sanarwa nan take a wannan rana, inda ya nemi hukumomin su yi bincike kan lamarin, domin cafke wanda ya aikata laifin tare da yin kira ga jama'ar kasar da su fahimci kalubalen da kasar ke fuskanta yanzu, tare da yin hada kansu. Haka kuma Shugaban ya yi kira ga shugabannin bangarorin daban daban da su yi shawarwari domin murkushe duk wata makarkashiyar da aka yi domin tada zaune tsaye da kawar da illa da rikicin ya jawo a kasar.

Haka shi ma firministan wucin gadi na kasar Najib Mikati ya yi jawabi ga bangarorin daban daban a kasar da dukkanin jama'ar kasar da su yi hakuri da juna domin kaucewa dauki mugun matakai kan tsoffin shugabanni, tare kuma da tsokanar juna ta yadda za a maido da shawarwari, da dukufa kan ceto kasar daga cikin mawuyancin hali a yanzu haka. Shugabannin jami'yyar Hezbollah da kungiyar Future Movement da dai sauransu sun ba da jawabi a wannan rana domin yin tir da wannan harin da aka kai. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China