Rundunar 'yan sanda a jihar Gombe dake arewa maso gabashin Nigeriya sun tabbatar da cewa, wassu 'yan bindiga sun harbi mutane biyu har lahira, suka kuma jikkata mutum daya a rukunin gidaje dake unguwar Ceceniya a jihar.
Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar Fwaje Atajiri ya tabbatar wa manema labarai, ya ce, harin ya faru ne a jiya Talata da misalin karfe 11 da minti 45 na tsakan dare, agogon Nigeriya.
Fwaje wanda ya bayyana harin a matsayin wani abin takaici, ya yi kira ga jama'a da su rika sanar da jami'an tsaro duk ayyukan da ba su amince da su ba, yana mai alkawarin cewa, akwai lada mai tsoka da aka ware domin biyan wadanda suka taimaka aka kama miyagun mutane a cikin al'umma.
Ya zuwa lokacin da wannan labarin ya iso mana, Mr. Fwaje ya ce, ba wanda ya dauki alhakin harin. (Fatimah)