Rahotanni daga Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya na cewa, sakamakon harin da aka kai a wani fitaccen otel da wassu motoci guda biyu makare da ababen fashewa, adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 11, sannan da dama sun jikkata.
Jiya ran 1 ga wata, motocin dai da suke makare da ababen fashewa sun tarwatse bi da bi a wajen otel din Jazeera, kusa da babban filin saukan jiragen sama dake Mogadishu, kuma otel din, an san shi da samun manyan baki daga jami'an gwamnati zuwa 'yan kasuwa.
Ya zuwa lokacin da rahoton ya iso mana, babu wanda ya dauki alhakin harin.
Firaministan kasar ta Somaliya Abdiweli Sheikh Ahmed, ya yi suka game da harin, ya ce, 'yan ta'adda sun fara a sabuwar shekarar bayan da tsohuwar shekara ta shude, suna ta aiwatar da kisan al'umma da tashin hankali. Hakan da suke yi sai ma ya kara hada kan kasar a kan su, amma ba ya raba ta ba.
Kungiyar Al-Shabaab dake da alaka da Al-Qaida ta sha arangama sosai da gwamnatin Somaliya da kuma sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU wato AMISOM. (Fatimah)