Rahotanni daga Maputo, babban birnin kasar Mozambique sun tabbatar da cewa, a kalla mutane 10 ne suka halaka a cikin hare-haren da jam'iyyar adawa ta Renamo ta kai cikin makonni 6 da suka gabata, mutane 26 kuma suka jikkata, a cewar ma'aikatar tsaron kasar.
Lokacin taron manema labarai a Maputo a ranar Laraban nan 4 ga wata, darectan tsare-tsare na ma'aikatar tsaro Cristovao Chume bai bayyana adadin asarar da rundunar tsaron kasar ta samu ba, ko kuma ita kanta jam'iyyar adawar ta Renamo, amma ya ce, kusan motoci 30 aka lalata lokacin harin.
Kusan duk hare-haren jam'iyyar ta Renamo suka abku ne a jihar tsakiyar kasar ta Sofala.
Harin baya bayan nan da Renamon ta kai shi ne a kan sansanin 'yan sanda a daren Talatan da ta gabata, da kuma wani dakin shan magani dake wani karamin gari na Tica a jihar Sofala, sai dai ba'a samu rahoton rasa rayuka, ko jikkata ba kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar ta sanar.
Zaman dar dar tsakanin jam'iyyar Renamo da gwamnati ya karu ne bayan da sojojin gwamnati suka kai samame a cikin tsaunuka na yankin Gorongosa a watan Oktoba, inda nan ne shugaban Renamon Afonso Dhlakama yake zama. (Fatimah)