Fashewar,wadda ita ce ta biyu cikin kwanaki biyu, ta faru ne da karfe 8 da mituna 25 na safe agogon birnin Moscow, lokacin da jama'a ke kokarin zuwa wuraren aiki ko makaranta
Ministar kiwon lafiya ta kasarRasha,Veronica Skvortsova wadda ta ke garin a lokacin da lamarin ya faru, ta ce an kwantar da mutane 3 a asibiti sakamakon munanan raunukan da suka ji.
Wakilian kamfain dillancin labarai na kasar Sin Xinhua da suka ziyarci wurin da lamarin ya faru,sun ce motar ta yi kaca-kaca,kana 'yan sanda sun killace wurin.
Bayanai na nuna cewa,motocin daukar marasa lafiya dana 'yankwana-kwana dana 'yan sanda gami da motocin ma'aikatar yanayin kota-kwana na kai gauro da mari a wurin da lamarin ya faru.
An sanar da shugaba Vladimir Putin game da mummar fashewar da ta faru,inda ake gudanar da bincike don tabbatar da ko hari ne na ta'addaci.(Ibrahim)