in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin 'yan gudun hijirar kasar Sham dake shiga Lebanon ya kai kimanin dubu 400
2013-04-02 16:24:55 cri

Hukuma mai kula da 'yan gudun hijira ta MDD wato UNHCR, ta ba da wani rahoto a birnin Beirut hedkwatar kasar Lebanon a ran 1 ga wata cewa, kawo yanzu, adadin 'yan gudun hijirar kasar Sham dake shiga kasar ya kai kimanin mutune dubu 400, adadin da ya karu da mutane dubu 25 bisa na mako da ya gabata.

Rahoton ya ce, ya zuwa karshen watan Maris, 'yan kasar Sham da suka tsere zuwa Lebanon, da Jordan, da Turkiya, da Iraqi, da kuma Masar, ya kai fiye da mutane miliyan 1.2, adadin ya karu da kashi 20 cikin dari bisa na farkon watan Maris.

Babban jami'i a hukumar Antonio Guterres, ya yi kiyasin cewa, ya zuwa karshen watan Yuni mai zuwa, adadin 'yan gudun hijira masu yin rajista a MDD wadanda za su tsere zuwa kasashen waje, zai kai fiye da miliyan 1.5, hakan ya sa ana bukatar dala miliyan 700 domin taimaka musu. Ban da haka, wannan jami'in ya yi kira ga kasashen duniya, da su ba da tallafi ga kasar Lebanon, da sauran kasashe domin taimaka musu wajen ba da kulawa ga 'yan gudun hijira. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China