Wasu alkaluma na baya-bayan nan da ma'aikatar lafiya ta kasar Libya ta bayar na nuna cewa, a kalla mutane 9 ne suka halaka, kana wasu 51 suka jikkata, a wani mummunan dauki ba dadi da ya faru ranar Litinin a garin Benghazi da ke gabashin kasar, tsakanin sojoji da mayakan Salafi na Ansar Al-sharia.
A cewar wani kwamandan soja, an kwashe wasu sa'o'i ana gwabza fadan, wanda daga bisani ya watsu zuwa garuruwan Al-Berka da Al-Salmani da ke makwabtaka da Benghazi, kuma fadan ya fi kamari ne da karfe 6 na safe, agogon wurin.
Bayanai na cewa, a ranar 11 ga watan Nuwamba ne, firaministan kasar ta Libya Ali Zeidan ya yi tattaki zuwa garin na Benghazi don tattauna sabbin matakan tsaron da aka dauka a yankin Cyrenaica da ke gabashin kasar, amma masu zanga-zanga suka yi ta masa ihu, abin da ya tilasta masa barin garin, inda suka dora masa laifi kan matsalar tsaron da ake fuskanta a birnin na tsawon watanni, lamarin da ya kai ga barkewar rikici.
A ranar 15 ga watan Nuwamban ma, garin na Benghazi ya fuskanci wani muumman tashin hankali, yayin da daruruwan masu bore suka bazama kan titunan babban birnin kasar, don nuna rashin jin dadinsu kan yadda masu dauke da makamai suka bude wuta kan gungun jama'a, inda suka halaka mutane 43, kana sama da mutane 460 suka jikkata. (Ibrahim)