in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sanda a Kenya sun ba da izinin neman wani da ake zargi da hannu a harin bas
2013-12-16 10:45:15 cri

Hukumar 'yan sanda a kasar Kenya a ranar Lahadin nan 14 ga wata suka fitar da takardar izini ta neman wani da ake zargin shi da hannu a harin da aka kai wa wani bas din fasinja da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 6 nan take, fiye da 30 kuma suka jikkata a ranar Asabar 13 ga wata a birnin Nairobi.

Babban Sefetan 'yan sandan kasar David Kimaiyo ya kuma hada da rarraba hotunan wanda ake zargin Hussein Nur Mohammed tare da kira ga daukacin al'umma da su taimaka da bayanai game da yadda za'a nemo shi domin ya fuskanci shari'a.

Mr. David Kimaiyo ya ce, an ambaci wadansu da ake zargi a wannan harin na ranar Asabar, a cikin su, har da sunan Hussein Nur Mohammed, 'dan shekaru 21 da haihuwa wanda tun da farko aka taba kama shi tare da sallame shi bisa sharadin zai rika zuwa kotu a kai a kai, ana ganin sa, sai dai bai cika wadannan alkawurra ba saboda bai sake bayyana kanshi a kotu ba.

Babban Sefetan 'yan sandan ya ce, abin da aka yi amfani da shi wajen kai hari ga wannan motar bas din mai mutane 32 a ciki da ke bin hanya ta 9 a birnin Nairobi ba gurneti ba ne, illa wani abin fashewa da aka shirya shi musamman, abin da ya bayyana shi a wani abin takaici da kuma shaida cewa, kasar ta Kenya har yanzu tana yaki da masu tsattsauran ra'ayi na addini da kuma kungiyar Al-Shabaab, don haka wajibi ne a kara sa ido da kuma mai da hankali wajen bincike da tsaurara matakan tsaro.

Wadannan kalamai na Mr. Kimaiyo sun zo ne bayan da adadin wadanda suka mutu sanadin wannan hari ya kai 6, kuma ana kyautata zato adadin zai karu bayan da 'yan sanda suka gano hannaye guda shida a wajen da harin ya auku.

Motar dai ta bangaren dama ta rabu da gangan jikinta bayan harin, sannan ya zuwa yanzu, babu wata kungiya ko mutum da suka dauki alhakin harin da ya bar tsoro da fargaba a zukatan al'ummar kasar ta Kenya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China