in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 2 sun rasa rayukansu sakamakon wani tashin hankali a Masar
2013-11-29 10:27:31 cri

Wata rigima da ta barke tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kirista Kibdawa a yankin Menya na kasar Masar, ta haddasa mutuwar mutane biyu, tare da raunata wasu mutane 10.

Kamar dai yadda wata kafar yanar gizo ta kasar ta bayyana, rikicin ya barke ne a ranar Alhamis 28 ga wata, sakamakon takaddama kan batun mallakar wani fili.

An ce, bangarorin biyu sun yi amfani da bindigogi domin kaiwa juna hari, lamarin da ya haddasa rasuwar mutum guda daga kowane bangare. A shekarar da ta gabata ma dai sai da aka hallaka mutane 5, tare da jikkata wasu 12 a wannan yanki, sakamakon dauki ba dadin da sassan biyu suka aiwatar. Tuni dai aka tura jami'an tsaro yanki da wannan lamari ya auku domin dawowa yanayin zaman lafiya, da kare ci gaban tashin hankali.

Mahukuntan kasar dai a baya na daukar matakan sasanta bangarorin ta hanyar tattaunawa da jagorinsu, da sauran masu ruwa da tsaki. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China