in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin AU ya yi tir da hari kan masu ba da agaji a Somaliya
2013-12-20 10:20:19 cri

Wakili na musamman na shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a Somaliya, Mahamet Saleh Annadif ya yi tir da kwantar bauna da aka yi a wajen birnin Mogadishu na kasar Somaliya ga masu ba da agajin kasa da kasa, inda aka hallaka 6, sannan 2 kuma suka samu rauni.

A cikin wata sanarwa da kungiyar tarayyar kasashen Afrikan AU ta fitar a ranar Alhamis din nan 19 ga wata, an ce, wannan harin ya faru ne lokacin da wadansu da ba'a sa ko su wane ne ba suka yi kwantar bauna ga wata mota dake dauke da likitoci masu ba da agaji da suka hada da guda 4 'yan asalin kasar Sham, da 2 kuma 'yan kasar ta Somaliya zuwa wani asibiti dake kusa da birnin na Mogadishu.

Likitocin kasar Sham su uku da likitocin kasar Somaliya su biyu da mai tsaron su guda daya, an kashe su nan take, sannan sauran likitocin su biyu suka ji rauni, kuma yanzu haka ana ba su jinya a asibitin Medina dake birnin Mogadishu.

A cewar sanarwar, Mahamet Saleh Annadif ya bayyana wannan danyen aiki da cewar tsoro ne da aikin rashin hankali, don haka, da kakkausar murya ya soki wannan harin na rashin imani a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, kuma ya ce, wannan harin ba zai dakushe kokarin da kungiyar take yi ba wajen ba da goyon baya ga al'ummar kasar ta Somaliya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China