in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An riga an gano mutanen da suka kai harin boma-bomai a Beirut, in ji kasar Lebanon
2013-11-24 17:08:21 cri
A ranar Asabar 23 ga wata, gwamnatin Lebanon ta yi shelar cewa, bayan yin bincike, an riga an gano mutane biyu da suka kai harin boma-bomai na kunar bakin wake a ofishin jakadancin Iran a Lebanon, wato dan Lebanon daya, da kuma dan Palestinu daya.

Kamfanin dillancin labaru na kasar Lebanon ya ambato kalaman alkalin kotun soja na Lebanon cewa, bayan yin bincike kan gawawwakin 'yan kunar bakin waken da suka mutu ta hanyar amfani da fasahar kimiyya ta DNA, an riga an tabbatar da cewa, daya daga cikinsu dan Lebanon ne mai sunan Mouin Abu Dahr, dayan kuma dan Palestinu ne dake zama a Lebanon mai suna Adnan Mussa al-Mohammad.(fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China