A ranar 9 ga wata, ma'aikatar harkokin wajen kasar Siriya ta ba da sanarwa, inda ta yi maraba da matsaya da kasashen Rasha da Amurka suka cimma game da batun Siriya, a sa'i daya kuma, ta yi kira ga kasar Amurka da abokan kawancenta da su daina ba da gudummawa ga bangaren adawa na kasar.
A ranar 9 ga wata, kakakin sakatare janar na M.D.D. Martin Nesirky ya ce, a wannan rana da safe, sakatare janar na M.D.D Ban ki-moon ya buga waya ga sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, domin nuna yabonsa kan yarjejeniyar da kasashen biyu suka daddale a ranar 7 ga wata game da batun Siriya. Nesirky ya ce, Ban ki-moon ya nuna yabo ga Kerry da Lavrov bisa himma da suka nuna kan wannan batu, kuma ya sa kaimi ga bangarorin da abin ya shafa da su yi amfani da wannan dama, don warware rikicin Siriya.
A gun taron manema labaru da aka saba yi a ranar 9 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin ta sa lura ga kasashen Rasha da Amurka da suka cimma daidairo a wasu fannoni game da warware batun Siriya ta hanyar siyasa, kuma kasar Sin tana maraba da hakan.
A wata sabuwa kuma, a birnin Damascus, yayin da shugaban kasar Siriya Bashar al- Assad ke zantawa da baki daga kasar Lebanon, ya yaba wa matsayin da jam'iyyar Hezbollah ta Lebanon ta tsaya a kai game da batun Siriya, kuma ya yi alkawari da samar da dukkan abubuwa gare ta. A ranar 9 ga wata da dare, babban sakataren jam'iyyar Hezbollah Hassan Nasrallah ya bayyana a birnin Beirut cewa, jam'iyyarsa tana shirin karbar dukkan makamai daga Siriya.(Bako)