in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An halaka mutane 40 a wasu hare-haren da aka kai a Najeriya
2013-11-27 10:38:30 cri

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Filato Felicia Anselm, ta tabbatar da cewa, wasu 'yan bindiga sun halaka mutane a kalla 40 a jihar Filato da ke yankin tsakiyar Najeriya, jihar da a baya ta yi fama da rikice-rikicen kabilanci da na addinin da suka lakume rayukan daruruwan jama'a.

Duk da cewa, kakakin 'yan sandan ta tabbatar da hare-haren da suka abku a karamar hukumar Barkin Ladi, inda mutane da dama suka rasa rayukansu, kana da dama suka jikkata, amma har yanzu ba a tabbatar da hakikanin adadin wadanda suka jikkata ba.

Ta ce, an kai hare-haren ne a cikin dare kuma a lokaci guda a garuruwa daban-daban wadanda suka hada da Foron, Gurabok, Rawuru da Tasu, wato karamar hukumar da ta kasance fagen daga tsakanin Fulani makiyayi da 'yan kabilar Berom.

Shi ma kakakin rundunar tsaron hadin gwiwa ta JTF da ke jihar ta Filato, Kyaftin Salisu Mustapha, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ta wayar tarho cewa, wasu 'yan bindiga ne da ba a san ko su wane ne ba suka kai hare-haren ranar Talata da misalin karfe 2 na dare, agogon wurin a kan kauyukan Katu Kapang, Daron, Tul da Rawuru da ke kananan hukumomin Barkin Ladi da kuma Mangu.

A cewarsa, maharan sun halaka kimanin mutane 13 a garin Katu Kapang, mutane 8 a kauyen Daron, mutune 9 a Tul, yayin da suka halaka sauran mutane 7 din a kauyen Rawuru. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China