in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikici a yankin arewacin kasar Lebanon ya haddasa mutuwar mutane sama da 10
2013-05-21 16:44:21 cri
A ranar 20 ga wata, aka shiga rana ta biyu na rikicin tsakanin magoya bayan gwamnatin Siriya da bangaren 'yan adawa na kasar a garin Tripoli da ke yankin arewacin kasar Lebanon, rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 3, tare da jikkatar wasu kimanin 40. Yanzu, haka kuma, rikicin na ci gaba da tsananta.

Wani jami'in tsaro da ya bukaci a boye sunansa a kasar Lebanon ya bayyana cewa, a ranar 20 ga wata, dakarun bangaren Alawis da ke goyon baya gwamnatin Siriya a yankin Jabal Mohsen dake birnin Tripoli sun yi musayar wuta da dakaru 'yan sunni da ke adawa da gwamnatin a yankin Bab al-Tabbaneh, daga bisani kuma, an ba da izni ga sojojin kasar Lebanon da su kara jibge sojoji a wurin da rikicin ya auku, don yin musayar wuta ga bangarorin biyu, abin da ya haddasa mutuwar soja 1, tare da jikkatar wasu mutane 9 ciki har da sojoji 6.

A ranar 20 ga wata, firaministan gwamnatin wucin gadi ta Lebanon Najib Miqati ya kira wani taron da ministan tsaron da ministan harkokin cikin gida na kasar, inda ya bukaci sojoji da rundunar tsaro su dauki kwararan matakai, don yaki da masu ta da zaune tsaye na Tripoli, da mayar da martani ga dakarun da suke harbin fararen hula.(Bako)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China