Kwamitin tsaron MDD ya yi tir da harin da aka kai harabar a ma'aikatar tsaron kasar Yemen da wani asibiti a jiya Alhamis 5 ga watan nan, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane 20, tare da jikkata wasu da dama.
Wata sanarwa daga ofishin kwamitin tsaron ta ce, akalla sojoji 20 ne suka rasu, baya ga wasu kusan 42 da suka samu raunuka, bayan da wani bam da aka dana cikin wata mota ya tarwatse da sanyin safiyar ranar ta Alhamis. Sanarwar ta kara da cewa, dukkanin wani nau'in ta'addanci abu ne da ba za a taba amincewa da halasinsa ba, kuma kwamitin na tsaro zai ci gaba da marawa gwamnatin kasar ta Yemen baya, a kokarinta na murkushe ayyukan ta'addanci.
Rahotanni daga rundunar tsaron kasar ta Yemen su ce, wasu mahara sanye da kakin soji sun kutsa kai cikin ma'aikatar tsaron, suka kuma yi musayar wuta da sojojin gwamnati, jim kadan da tashin bam din.
Tuni dai mahukuntan kasar suka dora alhakin aukuwar wannan hari ga kungiyar Al-Qaida, wadda suka ce, ita ce ke bayan duk wani yunkuri na tada kayar baya.
Tashe-tashen hankula a wannan kasa ta Yemen dai na dada ra'azzara, tun bayan kafa gwamnatin rikon kwarya, sakamakon juyin juya halin da ya haddasa kifar da gwamnatin shugaba Ali Abdullah Saleh a shekarar 2012. (Saminu)