Cikin jawabin nasa, Mr. Wang ya bayyana cewa, a halin yanzu, ministocin kasa da kasa suna taro a birnin Paris, ya kamata mu yi amfani da wannan dama mai kyau wajen cimma matsayi guda da kuma daukar matakai cikin hadin gwiwa domin ciyar da aikin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya gaba, da bude wani sabon shafi ga gamayyar kasa da kasa wajen ba da kokari kan wannan aiki.
Haka kuma, ya ce, domin cimma burinmu na shimfida zaman lafiya a yankin, kasar Sin tana sa kaimi da a fara aiwatar da manufofi guda uku, wadanda suka hada da:
Na farko, ya kamata a dakatar da musayar wuta a yankin, na biyu, ya kamata a tsayar da gina matsugunin Yahudawa a yakin, na karshe kuma, a soke takunkumin da aka kakaba wa yankin Gaza.
Daga bisani kuma, Wang Yi ya ce, a yayin da ake aiwatar da wandannan manufofi guda uku, a sa'i daya kuma, ya kamata bangarorin daban daban da abin ya shafa da gamayyar kasa da kasa su hada kai wajen ciyar da ayyuka guda uku gaba, watau da farko a nemi karin dama wajen inganta ayyukan shimfida zaman lafiya a yankin, sa'an nan, a tattauna kan yadda za a iya kiyaye sakamakon shawarwarin neman sulhu, a karshe kuma, a kafa tsarin kiyaye zaman lafiya yadda ya kamata.
Kaza lika, ya jaddada cewa, kasar Sin tana goyon bayan Falesdinawa da su farfado da ikonsu a ko da yaushe, tana kuma goyon bayansu wajen kafa kasa ta Falesdinu mai 'yanci bisa yankin iyaka da aka tsara a shekarar 1967, da kuma mai da birnin East Jerusalem a matsayin babban birnin kasar.
A karshe dai, Wang Yi ya nuna cewa, kasar Sin tana maraba da kuma nuna goyon baya ga dukkan kokarin da aka yi domin sassauta sabanin dake tsakanin Isra'ila da Falesdinu, ta yadda za a iya cimma burinmu na kafuwar kasashe biyu cikin zaman lafiya, da kuma dakatar da rikice-rikicen dake tsakaninsu, musamman ma asarar dukiyoyi da rayuka ga al'ummominsu. Muddin dai gamayyar kasa da kasa su ci gaba da dukufa kan wannan aiki, Falesdinu da Isra'ila su ci gaba da yin shawarwarin neman sulhu, tabbas ne za a sami kwanciyar hankali a wannan yanki. (Maryam)