A wannan rana a cikin wata sanarwa, mista Erekat ya bayyana cewa, Palestinu ta mika bukatarta ga mai shiga tsakani na musamman kan yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya na MDD mista Nickolay Mladenov.
Sanarwar ta ce, tun daga watan Satumbar bara zuwa yanzu, an kashe Palestinu 207 a yankunan Isra'ila. Don haka kamata ya yi kasashen duniya su yi bincike kai tsaye ba tare da wani bata lokaci ba. Kuma sanarwar ta kara da cewa, wadannan batutuwa na da alaka da juna. Dole ne kuma Isra'ila ta dauki alhakin hakan. Da zarar MDD ko sauran kungiyoyin duniya sun fara bincike, Palestinu za ta mika shaidu game da su. (Fatima)