Kaza lika, shugaba al-Sisi ya ce, a halin yanzu, akwai dama mai kyau wajen warware sabanin dake tsakanin Isra'ila da Falesdinu cikin zaman lafiya, duba da yadda bangarorin biyu suka amince da kokarin da gamayyar kasa da kasa suka yi wajen ciyar da shawarwarin neman sulhu a tsakaninsu gaba. A saboda haka, kasar Masar tana son yin aikin shiga tsakani domin taimaka wa bangarorin biyu wajen cimma nasarar shawarwarin neman sulhu dake tsakaninsu.
Bugu da kari, ya bukaci Isra'ila da Falesdinu da su yi shawarwari bisa ka'idojin yin hadin gwiwa da fahimtar juna, sabo da wannan ita ce kyakkyawar dama a gare su ta samun kwanciyar hankali, kyautata zaman rayuwar al'ummominsu da kuma habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu a nan gaba.
A jiya ne, firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fidda wata sanarwa, inda ya nuna maraba da goyon bayan da shugaban kasar Masar ya nuna wa Isra'ila da Falesinu wajen cimma nasarar shawarwarin neman sulhu dake tsakaninsu. (Maryam)