in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a ingiza taron wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa don kokarin sake farfado da shawarwari tsakanin Isra'ila da Falesdinu
2016-05-16 09:24:05 cri
Ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Marc Ayrault ya bayyana a jiya Lahadi cewa, Faransa za ta ci gaba da ingiza taron samar da zaman lafiya na kasa da kasa, don ganin sake farfado da shawarwari tsakanin Isra'ila da Falesdinu.

Ministan ya bayyana hakan ne, bayan da ya kammala ziyararsa ta yini guda a Falesdinu da Isra'ila. A yayin taron manema labarun da aka shirya a babban filin jiragen saman Ben Gurion dake birnin Tel Aviv, ya ce, ko da yake, Isra'ila ta kauracewa taron kasa da kasa kan samar da zaman lafiya da Faransa ta shirya, amma Faransa da kawayenta ba su daina yunkurin sake farfado da shawarwari tsakanin Isra'ila da Falesdinu ba. Ya ce, dole ne a shirya shawarwari kai tsaye tsakaninsu, amma wannan yunkuri yana fuskantar matsala.

Sabo da haka, ya kamata a ingiza shawarwarin. Wannan shi ya sa Faransa ta gabatar da wannan ra'ayi don sa kaimi ga bangarorin biyu su sake komawa teburin shawarwarin.

A bisa shiga tsakani da Amurka ta yi, a watan Yulin shekarar 2013, Isra'ila da Falesdinu sun farfado da shawarwarin da ya gamu da tsaiko har na tsawon shekaru 3, ko da yake akwai rarrabuwar kawuna game da batun sakin Falesdinawa da ake tsare da su, da batun gina matsugunan Yahudawa, lamarin da ya kai ga dakatar da shawarwarin a watan Afrilu na shekarar 2014.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China