Ban da haka kuma, rikici ya barke tsakanin 'yan sandan Isra'ila da Falesdinawa a sansanin 'yan gudun hijira na Shufat dake gabashin Jerusalem, haka kuma, zirga-zirga da tashe-tashen hankulan suna ci gaba da karuwa a wasu biranen Larabawa dake Jerusalem.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fidda wata sanarwa a ran 10 ga wata, inda ya sanar da cewa, gwamnatin kasar ta tsai da kudurin aike da karin 'yan sanda da dama zuwa Jerusalem, da kuma kara aike da 'yan sanda zuwa yankunan dake fi fama da rikice-rikice.
Bugu da kari, ya yi suka kan Falesdinu bisa zargin tayar da rikici.
Kana, yayin da shugaban Falesdinu Mahmoud Abbas ya yi shawarwari da ministan harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ta wayar tarho a ran 10 ga wata, ya bayyana cewa, ya kamata Isra'ila ta hana Yahudawa da su ci gaba da kai wa 'yan Falesdinawa hari bisa kariyar da sojojin suka yi musu. (Maryam)