Jiya ranar fursunoni ce ta kasar Palestinu. A wannan rana, Rami Hamdallah ya ba da sanarwa ga kasashen duniya da su ba da kariya ga iko da moriyar mutanen kasar da ake tsare da su a Isra'ila bisa dokoki, musamman ma yaran da ake iya lalata su cikin sauki.
Jiya a wurare da yawa dake yammacin gabar kogin Jordan da yankin Gaza, an yi zanga zangar goyon bayan mutanen Palestinu da ake tsare da su a gidajen kurkuku da sauran wuraren tsare da su a Isra'ila. Masu zanga zangar sun dauki hotunan fursunoni, tare da tutar Palestinu, domin bukatar Isra'ila da ta saki fursunoni da kyautata muhallinsu.
Bisa alkaluma masu dumi dumi da Palestinu ta bayar, an ce, kawo yanzu an tsare mutanen Palestinu kimanin dubu 7 a gidajen kurkuku 22 na Isra'ila, ciki har da yara 400. A bara, tun bayan tsanantar rikici tsakanin bangarorin biyu, Isra'ala ta cafke mutanen Palestinu kimanin 4800, mafi yawansu sun zo daga gabashin birnin Kudus da birnin Hebron dake yammacin gabar kogin Jordan.
A ranar 17 ga watan Afrilun shekarar 1974, Isra'ila ta saki Mahmoud Bakar Hijazi, wanda ya zama mutumin Palestinu na farko da bangarorin biyu suka yi musanyar fursunoni. Daga bisani, an dauki ranar 17 ga watan Afrilu na kowace shekara a matsayin ranar fursunoni ta Palestinu. (Fatima)