in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Faransa da Falasdinu sun bukaci maslaha game da batun Kudus
2015-09-23 11:03:51 cri
Shugaban kasar Faransa François Hollande da takwaransa na kasar Falesdinu Mahmoud Abbas sun yi kira da a kawo sassauci game da wurare masu tsarki dake tsohon gari na birnin Kudus.

Yayin zantawa da manema labarai bayan kammala shawarwari tsakanin shugaba Hollande da Abbas, shugabannin biyu sun yi kira da a kawo sassauci game da yanayin da ake ciki a birnin Kudus. Dan gane da batun bin ka'idar kiyaye zaman lafiya a yankin shugaba Hollande ya ce, Faransa za ta gabatar da shirin kafa rukunin kasa da kasa game da shawarwari tsakanin Falesdinu da Isra'ila a wajen taron M.D.D. da za a shirya nan ba da jimawa ba. Wannan rukunin bai tsaya kawai ga bangarorin 4 na batun Gabas ta tsakiya wato M.D.D., kungiyar EU, Amurka, da Rasha ba, kana zai hada da wasu kasashen Larabawa.

Abbas ya ce, shawarwarin su ne kadai za'a bi don samun zaman lafiya, a kullum alummar Falesdinawa na fatar a samu warware batun cikin lumana.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China