A yau Talata ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Rasha Sergei Lavrov a birnin Taschkent dake kasar Uzbekistan.
A yayin shawarwarin, Wang Yi ya bayyana cewa, kasashen Sin da Rasha sun kiyaye yin hadin gwiwa kan batutuwan kasa da kasa da yankuna, wadanda suka kasance muhimman bangare na tabbatar da ganin an aiwatar da manufofin kasa da kasa yadda ya kamata.
A nasa bangare, Lavrov ya bayyana cewa, kasar Rasha tana son hada kai da Sin don shirya ziyarar da shugaban kasar Rasha zai kai kasar Sin, da yin mu'amala kan kawancen tattalin arzikin Turai da Asiya da kuma shirin nan na "ziri daya da hanya daya".
Hakazalika kuma, Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin waje na kungiyar hadin gwiwa ta birnin Shanghai a birnin Taschkent a wannan rana. (Zainab)