Kana, ya ce, a halin yanzu, ana gamuwa da mawuyacin hali ta fuskar yunkurin siyasa tsakanin Falesdinu da Isra'ila, ana fatan kungiyar AU za ta iya samar da taimako kan wannan batu, domin ciyar da yunkurin zaman lafiya tsakanin Falesdinu da Isra'ila gaba, da kuma inganta kiran shimfida zaman lafiya na kasashen Larabawa, yayin dake kokarin aiwatar da dabarun mai da Falesdinu da Isra'ila a matsayin kasashe guda biyu a nan duniya yadda ya kamata.
Kaza lika, shugaba Abbas ya ce, goyon bayan da kungiyar AU ta baiwa Falesdinu cikin taruka daban daban, ya nuna damuwa da kulawar kungiyar kan batun Falesdinu, ya kuma nuna damuwarsa kan hare-haren ta'addanci da suke aukuwa a kasashen Afirka, ya ce, a halin yanzu, dukkanin kasashen duniya na gamuwa da kalubalen ta'adddanci, don gane da hakan, ya yi allah wadai da hare-haren da kungiyoyin ta'addancin suka kai a kasashen Mali, Burkina Faso, Kamaru da dai sauran kasashen Afirka. (Maryam)