A yau Litinin ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi tare da takwaransa na kasar Faransa Jean-Marc Ayrault sun gana da manema labaru a nan birnin Beijing, bayan kammala shawarwari .
Wang Yi ya ce kasar Sin na dora muhimmanci matuka kan batun Syria, kuma tana nuna goyon bayan ta ga bangarori daban daban na kasar, da su rungumi kuduri mai lamba 2254 na kwamitin sulhun MDD game da batun Syria, yana mai fatan bangarorin da batun ya shafa, musamman ma kasashen Rasha da Amurka, za su kara taka rawar da ta dace wajen tabbatar da tsagaita bude wuta, da daidaita batun Syria ta hanyar siyasa.
Bugu da kari, Mr. Wang ya yi kira ga bangarori biyu na kasar Syria, da su gudanar da shawarwari kai tsaye kuma a kan lokaci, domin cimma daidaito kan yadda za a daidaita batun Syria ta hanyar siyasa.(Lami)