Wang Yi ya bayyana cewa, kasashen Sin da Amurka za su gudanar da shawarwarin tattalin arziki da manufofi na sabon zagaye da yin mu'amalar al'adu a tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu, kana za su tattauna kan shirya taron koli na shugabannin kungiyar G20 da za a gudanar a birnin Hangzhou na kasar Sin.
Wang Yi yana fatan kasashen biyu za su ci gaba da yin hadin gwiwa, tare da warware matsalolin dake tsakaninsu, da kiyaye bunkasuwar dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata.
Har ila yau, Wang Yi yana fatan kasar Amurka za ta kiyaye manufar Sin daya tak, da martaba hadaddiyar sanarwa uku na Sin da Amurka, da warware batun yankin Taiwan yadda ya kamata.
A nasa bangare, Kerry ya bayyana cewa, kasar Amurka tana dora muhimmanci ga raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin. Kana Amurka ba ta canja matsayi kan batun yankin Taiwan ba, kuma ba za ta canja a nan gaba ba, sannan ba ta goyon bayan neman 'yanci yankin Taiwan.
Bangarorin biyu sun amince da ci gaba da yin mu'amala don warware matsalolin da ake samu a teku yadda ya kamata. (Zainab)