in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da Ban Ki-moon
2016-06-04 12:50:57 cri
Jiya Jumma'a 3 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da babban magatakardan MDD Ban Ki-moon a birnin Paris na kasar Faransa, inda aka gudanar da taron ministoci game da goyon bayan shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

A yayin ganawar tasu, Ban Ki-moon ya nuna juyayi matuka ga sojan kasar Sin mai aikin wanzar da zaman lafiya wanda ya rasu cikin harin ta'addanci da ya auku a kasar Mali, da kuma jajantawa ga sauran sojojin da suka jikkata. Haka kuma, ya sake yin allah wadai da harin din da 'yan ta'adda suka kai, ya kuma bayyana cewa, MDD za ta ci gaba da dukufa wajen kiyaye tsaron ma'aikata masu aikin wanzar da zaman lafiya a nan gaba.

A nasa bangare kuma, Wang Yi ya ce, kasar Sin ba za ta yi hakuri ko kadan ba kan masu aikata laifuffukan tashe-tashen hankula, za ta kuma ci gaba da halartar ayyukan kiyaye zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, da kuma cika alkawarinta na taimaka wa kasashen Afirka wajen kyautata kwarewarsu a fannin kiyaye zaman lafiya, yayin da daukar alhakinta yadda ya kamata a matsayin zaunanniyar mamba ta kwamitin sulhu na MDD. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China