in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Falesdinu ya jaddada shirin kafa kasashe 2 don samar da zaman lafiya da karko a yankin
2016-03-10 11:29:59 cri
Yayin da shugaban Falesdinu Mahmoud Abbas ke zantawa da mataimakin shugaban kasar Amurka Joseph Biden wanda ke ziyara a kasar, ya sake jaddada cewa, abu mai muhimmanci a kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki, shi ne tabbatar da iyakar da aka shata tsakanin Isra'ila da Falasdinu kafin yakin da sassan biyu suka gwabza a shekara 1967.

Abbas ya ce, kwace wasu yankuna da gina matsugunan Yahudawa da Isra'ila ta yi ita ce wani muhimmin dalilin da ya haddasa tashe-tashen hankali da rikicin zubar da jini na baya-bayan nan a yankunan. Ya jaddada muhimmanci da wajibcin yaki da ta'addanci, tare da nuna cewa, idan ana son yakar kungiyar IS, dole ne a kafa kasar Falesdinu da ke da hedkwata a Gabashin birnin Kudus.

Joseph Biden ya jaddada matsayin da Amurka ta tsaya na kafa shirin kasashen biyu, kuma ya bayyana cewa, Amurka ta dora muhimmanci game da gina matsugunan Yahudawa da Isra'ila ta yi.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China