Netanyahu ya bayyana hakan ne yayin taron majalisar ministocin kasar, yana mai cewa gwamnatin hadakar kasar na ganin cewa ya zama dole a fadada majalisar ministocin kasar. Bayan gudanar da gyare-gyare ga gwamnatin, Isra'ila za ta ci gaba da dukufa ka'in da na'in wajen cimma burin samar da zaman lafiya ga al'ummar Falesdinu ta hanyar diplomasiyya a karkashin taimakon sauran kasashe.
A ranar 17 ga watan nan ne, shugaban kasar Masar Abdel Fattah Al-Sisi, ya bayyana cewa yanzu haka, akwai damar warware batun samar da zaman lafiya tsakanin Falesdinu da Isra'ila cikin ruwan sanyi, kuma kasar Masar na fatan taka rawar gani a shawarwarin, don cimma nasararsu, matakin da kuma Netanyahun ya yi maraba da shi.
A wata sabuwa kuma, a daren ranar Asabar, firaministan kasar Faransa Manuel Walls ya isa kasar Isra'ila, don fara ziyarar aiki ta yini uku a yankunan Falesdinu da Isra'ila. A kuma Litinin din nan Mr. Walls din zai yi shawarwari da Netanyahu, da shugaban Falesdinawa Mahmud Abbas, a wani mataki na karfafa shawarwari tsakanin Falesdinu da Isra'ila.(Bako)