in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kafa dokoki biyar tare da gyara kan dokoki 37 a shekarar 2015
2016-03-09 19:33:34 cri

An yau din nan Laraba ne shugaban kwamitin majalissar wakilan jama'ar kasar Sin Mista Zhang Dejiang, ya gabatar da rahoton aikin kwamitin, inda cikin sa ya bayyana cewa a shekarar bara, Sin ta gabatar da dokoki guda biyar, yayin da kuma ta yi gyara kan dokoki 37.Baya ga wadannan, an gabatar da wani kuduri dangane da wata matsalar shari'a.

A bangaren kafa dokar tsaron kasa kuwa, kwamitin ya mai da muhimmanci sosai kan kafa dokar tsaron kasar, kuma an zartas da ita bayan bincike uku da aka gudanar. Ban da wannan kuma, Sin ta zartas da dokar yaki da ta'addanci a watan Disamba na shekarar bara, don tabbatar da manyan ka'idojin da Sin take bi wajen yaki da ta'addanci.

A bangaren dokokin da suka shafi zaman rayuwar jama'a kuwa, kwamitin ya kyautata dokoki masu alaka, inda ya gyara dokar hana gurbata iska. Dadin dadawa, Sin ta gyara dokar ingancin abinci don tinkarar wasu matsalolin da suka bullo a wannan fanni. A sa'i daya kuma, Sin ta kafa dokar yaki da nuna karfin tuwo cikin iyalai, da gyara dokar yawan mutane da kayyade haihuwa. Kaza lika an fara aiki da dokar ba da iznin haifuwar yara biyu daga ran 1 ga watan Jarairu na bana.

Bugu da kari, kwamitin ya zartas da gyararren shirin tsarin dokokin hukunta manyan laifuffuka don kyautata shi yadda ya kamata. Ban da wannan, kwamitin ya kuma kafa dokar binciken sararin dake karkashin teku da bunkasa albarkatun sa, sannan da gyara wasu dokoki, ciki hadda dokar tallace-tallace, da dokar samar da irin shuka, da dokar sa kaimi ga yin amfani da fasaha da kimiyya don samun bunkasuwa. Sai kuma dokar ba da ilmi da dai sauransu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China