Babban direktan kamfanin yin amfani da makamashin nukiliya ta kasar Sin Sun Qin ya ce, bisa manufar kamfanin ta habaka aikin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya a kasashen ketare, kasar Sin tana kokarin gina tashoshi 30 masu aiki da makamashin nukiliya wajen samar da wutar lantarki a kasashen da ke yankin nan na "zirin daya da hanya daya" kafin shekarar 2030.
Yanzu haka wannan kamfanin na kasar Sin ya daddale yarjejeniya da kasashen Argentina, Brazil da sauran kasashe da dama. Sun Qin ya kara da cewa, kamfaninsa zai ci gaba da habaka batun samar da wutar lantarki ta hanyar makamashin nukiliya a kasashen Argentina, Pakistan, Aljeriya, da Birtaniya, sa'an nan zai mai da hankali wajen raya wannan fasaha a kasuwannin kasashen Latin Amurka, Asiya da Afirka, har ma da kasashen Turai. (Tasallah Yuan)