A cikin rahoton aikin gwamnatin kasar Sin da ya gabatar a yayin taron cikakken zama na 4 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC a yau Asabar 5 ga wata, firaministan kasar Li Keqiang ya ce, nan da shekaru 5 masu zuwa wato yayin da kasar Sin take aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13, tilas ne a sa muhimmanci kan fannoni 3, a kokarin ganin kasar ta zama kasa mai zaman wadata a dukkan fannoni.
Da farko, a mayar da samun bunkasuwa a gaba da kome. Na biyu kuma, a kara karfin yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki, daga karshe dai, a gaggauta sabunta karfin kasar ta fuskar raya tattalin arziki.
Nan da shekaru 5 masu zuwa, jama'ar kasar na da imani sosai wajen samun nasarar ganin, kasar Sin ta zama kasa mai zaman wadata, inda jama'ar kasar suka kara jin dadin zamansu, ana kara fuskantar makoma mai kyau wajen raya sha'aninmu mai halin musamman na gurguzu. (Tasallah Yuan)