in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
manufar tsarin iyalai na kasar Sin ba za ta canja a kwana kusa ba
2016-03-08 20:04:19 cri
Shugabar hukumar lafiya da tsarin iyali ta kasar Li Bin ta bayyana cewa, manufar tsarin iyali ta kasar Sin ba za ta canja a kwana kusa ba.

Li Bin wadda ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a gefe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar da ke gudana yanzu haka a nan birnin Beijing, ta kuma ce a yanzu haka babu wasu shirye-shirye da aka tsara game da sassauta wannan manufa.

Li ta ce, idan har albarkatun da ake da su ba su yi dai-dai da yawan al'ummar kasar ba, to ba za a canja wannan manufa ba.

Alkaluma na nuna cewa, a shekarar 2015, yawan Sinawa ya kai biliyan 1 da miliyan 375, idan aka kwanta da yawan al'ummar Amurka miliyan 320, kasar da ke kan gaba ta fuskar tattalin arziki.

A wannan shekarar ce dai mahukuntan kasar ta Sin suka baiwa ma'aurata iznin haifar 'da fiye da guda. Matakin da ya sassauta dokar nan ta 2013 da ta baiwa ma'aurata damar haifa 'ya'ya na biyu, idan iyayensu su kadai ne a wajen nasu iyayen.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China