A wannan rana ne dai aka gudanar da taron wakilan al'ummar lardin Zhejiang mahalarta taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, domin nazartar daftarin shirin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma na shekaru biyar biyar a karo na 13. Mista Wang Yi da ya zo sauraron muhawarar ya bayyana cewa, Afirka ta zama muhimmiyar nahiya wajen hadin gwiwa da Sin, musamman ma a fannin masana'antu. Kasashen Afirka su ma sun gano cewa, bai kamata su nemi samun bunkasuwa bisa albarkatunsu kadai ba, wato dole ne su kara saurin kafa masana'antu, da raya tattalin arzikinsu ta hanyoyi daban daban. A sabili da haka, hanyar da Sin ke bi ta yin hadin gwiwa ta yi matukar dacewa da bukatunsu. (Fatima)