in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirye-shirye goma na hadin gwiwar kasar Sin da Afirka sun dace da zamanin da ake ciki
2016-03-08 13:05:29 cri

A yau Talata ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa cikin shekaru 60 da cikar huldar diplomasiyya tsakanin Sin da kasashen Afirka, duniya na canzawa, kana kasar Sin da kasashen Afirka su ma sun sauya matuka, amma duk da haka dankon zumunci a tsakanin sassan biyu ba zai canza ba, hakan kuma ya sa bangarorin biyu su kara amincewa da juna, da kuma mara wa juna baya.

Mr. Wang Yi ya bayyana hakan ne a nan birnin Beijing, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin cinikayya, a yayin taron manema labaru da aka shirya. Ya ce a karshen shekarar bara, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sanar da manyan shirye-shirye goma na hadin kan Sin da Afirka. Ya ce wannan shiri na iya tinkarar sabon kalubalen da ci gaban Afirka ke fuskanta sakamakon sauyawar yanayin tattalin arziki da duniya ke ciki, don haka shirin ya yi matukar dacewa da zamanin da muke ciki.

Kawo yanzu dai, Sin ta riga ta tuntubi kasashen Afirka fiye da 20, a kokarinta na aiwatar da sakamakon da aka samu, a yayin taron koli na Johannesburg na dandalin FOCAC.

Bugu da kari, Wang Yi ya kara da cewa, a wadannan shekarun da suka gabata, akwai jita-jita kan hadin gwiwar Sin da Afirka. Amma Afirka ce kadai ke da ikon magana kan hakan. Duk da haka, a yayin taron koli na bara na FOCAC, dimbin shugabannin kasashen Afirka sun yi tsokaci da cewa, kasar Sin ba ta taba yin mulkin mallaka a Afirka ba. A maimakon haka, Sin ta kan tallafawa Afirka wajen fita daga kangin talauci domin neman samun bunkasuwa. Ya ce ko da yaushe Afirka na neman wata aminiyar hadin kai da ke da moriyar bai daya tare da ita, kuma kasar Sin ita ce wadda Afirkan ke nema. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China