Shugaban wanda ya zanta da wakilan al'ummar lardin Heilongjiang yayin taron majalisar wakilan jama'ar duk kasa dake wakana yanzu haka a nan birnin Beijing, ya bukaci wakilan da su maida hankali ga lalubo hanyoyin samar da ci gaba, ta hanyar kirkire-kirkire bisa tsari, irin wadanda ba sa cutar da muhalli, wadanda kuma za su haifar da ci gaba na bai daya.
Mr. Xi jinping ya kara da cewa ya zama wajibi wakilan kananan hukumomi, da wakilan jam'iyya, su yi riko da dokokin kasa a yayin da suke aiwatar da sauye-sauye, a kuma gabar da suke nusar da sauran al'umma da aiwatar da hakan.
Ya ce ya dace a ci gaba da daga matsayin jami'an da suka nuna kwazo, gaskiya da rikon amana, a matsayin hanyar karfafa gwiwar su.