in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta rika kokarin kiyaye zaman lafiya a tekun Nanhai
2016-03-08 12:32:13 cri

An yi taron manema labaru na taro karo na 4 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 12 a yau Talata, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya bayyana a yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru cewa, a matsayin kasa mafi girma a bakin tekun Nanhai, kasar Sin ta fi son tabbatar da 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a tekun. Kasar Sin ta rika kokarin kiyaye zaman lafiya a yankin.

Wang Yi ya jaddada cewa, 'yancin zirga-zirga ba 'yancin gudanar da dukkan ayyukan da ake so ba, kasar Sin ba za ta yarda ko wata kasa dake da nufin tada rikici a yankin ba, sauran kasashen dake wannan yanki su ma ba za su yarda haka ba.

Bugu da kari, Wang Yi ya jaddada cewa, kafa ayyukan kare kai a tsibiran da kasar Sin ke da ikon mulki ya dace da dokar duniya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China