Ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya bayyana a yau Talata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ba za ta habaka karfinta a kasashen waje kamar yadda wasu manyan kasashen duniya suka yi ba, kana ba za ta sa baki kan harkokin siyasa na sauran kasashen duniya ba. Za ta nemi wata hanyar kiyaye moriyarta da ta fi samu karbuwa daga bangarori daban daban.
An yi taron manema labaru na taro karo na 4 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 12 a yau, inda minista Wang ya amsa tambaya game da kasar Sin ke kafa sansanin samar da guzuri ga sojoji a kasar Djibouti, ya ce, kamar yadda sauran kasashen duniya, kasar Sin tana kara samun moriya daga kasashen waje.
Wang Yi ya kara da cewa, na farko, kasar Sin tana son kara daukar nauyin harkokin tsaro na kasa da kasa. Na biyu, tana son biya bukatun wasu kasashen da kasar Sin ke samun moriya daga wajensu, kuma tana kwada kafa manyan ayyukan more rayuwa da ba da tabbaci a wadannan kasashe. Na uku, Sin tana son karfafa hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya, ciki har da hadin gwiwa a fannin tsaro, kana tana kokarin shiga aikin daidaita manyan batutuwan duniya ta hanyar siyasa, domin kyautata muhallin tsaro ga bunkasuwar kasar Sin a kasashen waje.(Lami)