in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta gabatar da fasalin shirin shekaru biyar-biyar karo na 13
2016-03-06 13:42:26 cri

A yau ne aka kira taron manema labaru karo na farko na taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka bude jiya Asabar a nan birnin Beijing, inda aka gayyaci darektan hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin Mista Xu Shaoshi, don ya gabatar da yanayin bunkasuwar tattalin arziki da al'ummar Sin da kuma fasalin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13.

Mista Xu ya ce, tun shekarar da ta gabata duniya ke fuskantar mawuyacin hali na raya tattalin arziki, kuma Sin ma ta fuskanci kalubalen koma bayan tattalin arziki, amma a karkashin jagorancin kwamitin tsakiyar jam'yyar JKS da majalisar gudanarwa ta kasar, Sin ta ci gaba da bin hanyar samun bunkasuwa mai dorewa, da kyautata tsare-tsare da take aiwatar a fannoni daban-daban yadda ya kamata, saboda haka, tattalin arzikin Sin na samun bunkasuwa da ya dace.

Ban da wannan kuma, Mista Xu ya kara da cewa, an tsara shirin raya kasa da zaman al'umma na shekaru biyar-biyar a karo na 13 bisa shawararin da kwamitin tsakiya ya bayar karkashin manufofin zurfafa kwaskwarima, musamman ma kan yadda ake mai da hankali wajen daidaita alakar dake tsakanin gwamnati da kasuwa, don yin amfani da fifikon kasuwani wajen rarraba albarkatu. A sa'i daya kuma ya ce, ya kamata a kara hada kai tsakanin kasuwa da gwamnati don tabbatar da shirye-shirye da tsare-tsaren da JKS ta bullo da su. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China