Ministan ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin Miao Wei ya ce, Sin ta zama kasa mafi karfi a duniya wajen samar da kayayyakin yada bayanai na latironi, inda yawan kudin da kasar ta samu a wannan fanni ya kai dala biliyan1240, yayin da kuma yawan kudin da suka shafi sashen shige da fice a wannan fanni ya kai dala biliyan 133, adadin da ya kai kaso 32 bisa dari, na daukacin kudin da kasar ta samu a cinikayyar shige da fice a shekarar bara.
Har illa yau Mr. Miao ya ce, masana'atun kera na'urorin yada bayanai na latironi, na gudanar da sana'a ce da ke da fifikon samun ci gaba, a fannin kirkire-kirkire, masu kuma samun fifikon ba da jagoranci da samun yaduwa. Haka zakila kasashen duniya na dora matukar muhimmanci a kan wannan sana'a a kokarin neman samun ci gaba da yin takara a daukacin duniya.
Ya ce Sin ta riga ta zama kasa mai karfi a fannin samar da kayayyakin yada bayanai na latironi, ta samu ci gaba mai armashi ta fuskar kimiyya da fasahohi a fannoni da dama ciki hadda sadarwa, musamman bangaren na'urorin kwamfuta na zamani, da akwatunan telibiji na zamani da dai sauransu.
Sai dai duk da haka, akwai matsaloli dake yiwa bunkasuwar masana'atun kera na'urorin yada bayanai na latironi na kasar Sin tarnaki, idan an kwatanta da sauran kasashen duniya, saboda ganin Sin ba ta mallaki wasu fasahohi masu tushe a wannan fanni ba. Mr. Miao ya yi nuni da cewa, ma'aikatarsa za ta fidda wasu sabbin manufofi da za su kyautata fasahohin sadarwa, tare kuma da nuna goyon baya ga ayyukan kirkire-kirkire a wannan fanni a nan gaba. (Amina)